Barka Da Warhaka
  • Sarewa Radio
9 episodes
Barka da Warhaka, shiri ne da ke sakarwa matasa linzamin bayyana ra’ayinsu a siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da sauran batutuwan rayuwa ba tare da takunkumi ba. Zamani...riga

Episodes

Barka Da Warhaka: Episode 8 Balkisu Aliyu Mai Kilishi
2020 Aug 231h 45m 26s
Kilishi, wani abincine na kasaita a kasar Hausa, wanda yake da sunaye daban daban misali a turanci ana kiransa da "Beef Jerky". Kasan cewar Amurka bata bari a shigo da nama Hausawa mazauna yammacin duniyar na fama da rashin Kilishi, Hakan yasa Balkisu Aliyu mai kamfanin Alsutra Kitchen ta fara yin Kilishin ana saida shi a kasashe da dama. Hakan yasa muka gayyato ta shirin Barka da Warhaka don tattaunawa da ita.
Barka Da Warhaka: Episode 7 Freiiboi
2020 Aug 1152m 11s
A yau mun zanta ne da Sani TY Sha'aban wanda aka fi sani da Freiiboi mawaki dan shekaru 15, kan irin burin shi a rayuwa da kuma irin gatan da yasamu na tallafi da kuma kwarin gwiwa daga waurin mahaifinsa.
Barka Da Warhaka: Episode 6 Abdul Amdaaz
2020 Aug 0946m 40s
A yau mun tattauna da mawakin zamani Abdul Amdaz wanda ke rera waka da salon Hausa Sudaniyya.
Barka Da Warhaka: Episode 5 Lawal Abdullahi Matazu
2020 Aug 091h 43m 7s
Shin ko yawaitar sabbin wayoyin hannu na zamani ya kashewa masu sana'ar daukan hoto kasuwa? Mun tattauna da Lawal Abdullahi Matazu, Mai daukan hoto, gami da zayyanar rubutu (Graphics designing) inda ya warware mana zare da abawa.
Barka Da Warhaka: Episode 4 Menene Podcast
2020 Aug 081h 39m 38s
A yau munyi duba ne kan Podcast, ma'anarsa da tarihinsa da kuma bukatar karbuwarsa a wurin matasa musamman masu magana da harshe Hausa a fadin duniya.
Barka Da Warhaka: Episode 3 TY Sha'aban (Shaba)
2020 Jul 301h 28m 3s
Ba 'boyayyen abu bane mafi yawancin iyaye basa tallafawa yaransu wajen kara musu kwarin gwiwa a bangaren wasanni da hikimomi na yau da gobe. TY Sha'aban wanda aka fi sane da (Shaba) ya bambamta da sauran iyaye domin kuwa shi yana tallafawa dansa (Freiiboi) wajen yin wakokin zamani. Ko me yasa? ku biyo mu cikin shirin Barka da Warka domin jin dalili.
Barka Da Warhaka: Episode 2 Matsalar Fyade
2020 Jul 292h 27m 48s
Matsalar fyade, matsala ce da ta zama ruwan dare musaman a arewacin Najeriya, inda a yan kwanakin nan rahotanni suka yawaita akan fyade musamman ga kana nan yara maza da mata har ma da jarirai. Saboda haka ne a cikin wannan shirin muka gayyato Fakhriyya Hashim 'Yar rajin kare hakkin mata tare da Saratu G Abdullahi, Malamar Jinya da kuma rajin kare hakkin mata domin tattaunawa akan wannan matsala. Asha sauraro lafiya.
Barka Da Warhaka: Episode 1 Musgunawa Bakaken Fata
2020 Jul 2929m 54s
A cikin shirin "Barka da Warhaka" kashi na farko mun gayyato Maryam Bugaje, 'Yar Jarida kuma mai fashin bakin akan lamuran yau da kullum inda muka tattauna game da zanga zangar da ta barke a Amurka sakamon cin zarafin bakaken fata da jami'an 'Yan sanda ke yi a Amurka.
Barka Da Warhaka "Tallan Shirin"
2020 Jul 231m 35s
"Barka da Warhaka", shiri ne da ke sakarwa matasa linzamin bayyana ra’ayinsu a siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da sauran batutuwan rayuwa ba tare da takunkumi ba. Zamani...riga